AN BUKACI MAWADATA DA SU RIKA TALLAFAWA MABUKATA A WATAN RAMADHAN..

Kungiyar bunkasa ilimi da harkokin demokradiyya ta SEDSAC, ta yi kira ga masu wadata a cikin al’umma su rinka tallafawa mabukata da kayayyakin abinci domin rage masu radadi musamman ma a wannan watan na Azumin Ramadana.
Cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar Comrade Hamisu Kofar Na’isa, ta ce bada tallafin nada matukar muhimmanci la’akari da dinbin ladan dake cikin wannan wata mai alfarma.
Sanarwar ta yi kira ga ‘yan kasuwa da suji tsoron Allah wajan kaucewa Karin farashin kayayyaki musamman ma a wannan watan mai alfarma, lamarin data ce zai baiwa masu karamin karfi sukunin sayan kayayyakin masarufi ba tare da kuntata ba.
Sanarwar ta yaba da shirin ciyarwa da gwamnati ke yi da shekaru da dama da suka gabata, kana kuma ta yi addu’ar dan samun tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a wannan watan mai albarka.

en_USEnglish
en_USEnglish