AN RUFE KWALEJIN NAZARIN AIKIN TSAFTA DA KIWON LAFIYA.

Hukumomin kwalejin fasahar aikin tsafta da kiwon lafiya ta Kano sun kulle makarantar.

Rahotanni sunce hukumar kwalejin ta dauki wannan mataki ne domin nuna goyon baya ga kungiyar ma’aikatan lafiya daba likitoci ba wanda suka shiga mako na uku suna gudanar da yajin aiki.

Wannan mataki daliban kwalejin sunyi carko-carko bayan da suka isa harabar makarantar domin shiga lakca.

A ziyarar da wakilin gidan radion dala ya kai da safiyar yau ya iske kofar makarantar a garkame tare da ganye a jikin ta,hakan ya sanya yaji ta bakin daliban game da wannan lamari

Wakilinmu Abba Isa Muhd yayi kokarin tuntubar hukumar kwalejin, amma lamarin ya ci tura.

sai dai wakilin namu ya samu tattaunawa da wasu daga cikin daliban makarantar wadanda ke tsaye a kofar makarantar,inda suka bayyana rashin jin dadinsu game da wannan mataki.

 

 

en_USEnglish
en_USEnglish