HUKUMAR HANA FASA KAURI TAYI GARGADI GA YAN SUMOGA.

Hukumar hana fasa kauri ta kasa Custom ta gargadi ‘yan sumoga da su guji yiwa tattalin arzikin kasar nan zagon kasa.

Kwanturolan hukumar kwastan dake kula da shiyyar yammacin kasar nan Muhammad Uba ne yayi wannan kiran yayin ganawa da manema labarai a jihar Legas.

Gargadin na kwastan na zuwa ne biyo bayan kayayyakin da suka kama, wanda suka hada da motoci da tsofaffin tayoyi da buhun shinkafa guda 5516 da aka kiyasta kudinta akan Naira miliyan 76.5

Kamun ya zo ne a makon da Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayyana cewa gwamnati ta daina shigo da shinkafa daga kasashen ketare.

en_USEnglish
en_USEnglish