MASU GARKUWA DA MUTANE SUN SACE MATAN WANI ATTAJIRI A JIHAR KADUNA.

Wasu ‘yan Bindiga sun yi garkuwa da matan wani dan kasuwa a karamar hukumar Birnin Gwari da ke cikin jihar Kaduna.

‘Yan bindigar sun kai harin ne a garin Maganda cikin dare kafin wayewar safiyar Lahadi suka sace matan Alhaji Ado Nakwana guda uku.

Wani makusanci ga dan kasuwar ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun shiga kauyen kusan karfe biyu na dare, kuma kai tsaye suka isa gidan dan kasuwar suka bude wuta a kofar gidansa.

Ya ce “sun tafi da matansa guda uku bayan ba suyi katarin samun sa ba, domin kuwa ya ranta a na kare lokacin da suka shiga gidan.

Amma daga baya sun sako daya daga cikin matan tare da ba ta sakon numbar waya ta kawo wa mijinta.

Ya zuwa yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna bata kai ga cewa komai ba dangane da batun.

Wannan na zuwa a yayin da wasu rahotanni suka ce ‘yan bindiga sun kaddamar da hari a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna inda suka sace wani direba kafin daga bisani ya tsere daga hannunsu.

Yankin Birnin Gwari a Kaduna na cikin yankunan arewa maso yammaci da ake yawan samun matsalar sace-sacen mutane domin kudin fansa.

 

en_USEnglish
en_USEnglish