ANYI KIRA GA MAWADATA DA SU RIKA TALLAFAWA MABUKATA.

Guda cikin shugabannin kungiyar cigaban al’umma ta unguwar Hausawa zoo road wato zuda , Hassan Malam yayi kira ga kungiyoyi da mawadata da su rinka ciyar da mabukata , don rage musu radadin halin kaka nikayin da suke ciki.
Hassan Malam yayi wannan kiran ne , lokacin da kungiyar ta raba kayan abinci ga wasu mabukata a ofishin kungiyar.
Ya ce, raba abinci ga mabukata zai taimaka kwarai wajen saka musu farin ciki da walwala a zukatan su.
Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin sun bayyana jin dadin su.
Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewa, sama da mutane 50 ne maza da mata suka samu tallafin kungiyar.

en_USEnglish
en_USEnglish