GWAMNATIN JIHAR KANO NA YUNKURIN FARFADO DA MASANA’ANTUN DA SUKA DURKUSHE A JIHAR KANO.

Gwamnatin jahar Kano ta nanata kudirin ta na farfado da kamfanonin da masana’antun da suka durkushe a jihar Kano.

Kwamishinan kasuwanci, da jam’iyyun gama kai da yawon bude ido Alhaji Ahmad Rabi’u ne ya bayyana haka yayin wani kwarya-kwaryan taro da masu ruwa da tsaki akan harkokin kasuwanci na Kano wanda ya gudana a ofishinsa

Alhaji Umar Dangote, guda cikin wadanda suka halarci taron yace wajibi ne a tattauna da masu kamfanin domin fayyace matsalolin da suka sabbaba durkushewar kamfanonin nasu.

Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewa, fiye da kamfanoni 200 ne basa aiki a fadin jihar nan.

en_USEnglish
en_USEnglish