PDP TA KALUBALANCI SHUGABA BUHARI YA WANKE KANSA DAGA ZARGIN BADAKALAR KUDADEN TALLAFIN MAI

Jam’iyyar PDP ta zargi shugaba Muhammadu da hannu dumu-dumu wajen tafiyar da harkokin tallafin albarkatun mai da gwamnatin tarayya tace ta biya a kwanakin baya da aka fuskanci karanci a kasar nan.
A ‘yan kwanakin da suka gabata ne , karamin minister a ma’aikatar kula da albarkatun mai Mr Ibe Kachikwu ya sanar da cewa, gwamnatin tarayya na kashe naira trillion daya da billion hudu a duk shekara wajen biyan tallafin mai ga ‘yan kasa.
Kalaman ministan sun zo ne shekaru uku bayan da gwamnatin tarayya ta ambata cewa, ta soke tsarin bada tallafin mai
A cikin wata sanarwa da sakataren Labarun PDP Kola Ologbondiyan ya fitar jiya lahadi, Jam’iyyar ta kalubalancin shugaba Muhammadu Buhari ya mika kansa ga tsarin bincike na hakika kan yadda aka sarrafa wadancan kudade naira trillion guda da billion 4 da gwamnati tace ta kashe da sunan tallafin mai ga ‘yan kasa.
Haka kuma PDP ta bukaci shugaba Buhari ya wanke kansa daga zargin almundahanar kudade da ake zargin an aikata a hukumomin gwamnati daban daban musamman wadanda ke samar da kudaden shiga ga gwamnati.
Jam’iyyar ta PDP inji sanarwar, kamata ya yi ‘yan najeriya su lura cewa, matakin gwamnonin najeriya na bukatar gudanar da binciken kwakwaf akan hada-hadar tallafin mai tun daga shekara ta 2015 zuwa bana na kara haska hannun shugaba Buhari cikin zargin almundahanar tallafin, musamman la’akari da matsayin sa na babban ministan albarkatun mai na kasar nan.
Idan za’a iya tunawa, kafin zabar sa a matsayin shugaban najeriya a shekara ta 2015, Janar Buhari ya sha aibata tsarin gwamnatin tarayya ta wancan lokaci na bada tallafin mai ga ‘yan kasa, al’amarin daya bayyana a matsayin hanyar sace dukiyar kasa.

en_USEnglish
en_USEnglish