WASU KUSOSHIN APC A KATSINA SUNYI BARAZANAR FICEWA DAGA JAM’IYYAR.

Uku daga cikin masu neman Jam’iyyar APC ta basu takarar gwamna a jihar Katsina sunyi barazanar fita daga Jam’iyyar saboda abinda suka kira rashin adalci a yayin zaben shugabannin Jam’iyyar da aka gudanar shekaran jiya asabar.
Sanata Mohammed T. Liman da Dr Usman Bugaje da kuma Alhaji Sa’idu Ilu sun bayyana hanyar da akayi zaben a maytsayin abain kyama.
A cikin wata sanarwa da suka fitar, kusoshin jam’iyyar ta APC A JIHAR Katsina sunyi barazanar fita daga Jam’iyyar biyo bayan watsi da kiraye-kirayen da sukayi na cewa, lallai a gyara kura-kuran da akayi a yayin zaben shugabannin na APC a jihar.
Sunyi ikrarin cewa, an ci zarafin dimokaradiyya a APCn Katsina la’akari da sigar da aka bi wajen zaben shugabannin.
Sunce yadda zaben ya gudana abin kunya ne ga kasa da kuma ‘yan najeriya dake zaune a gida da kasashen ketare, la’akari da yadda aka salwanta rayukan mutane tare da jikkata wasu a sassa daban daban na kasar nan.
Dr Usman Bugaji da Sanata T. Liman da kuma Alhaji Sa’idu Ilu, sunce ba’a sayar da takardun tsayawa takara ba ga galibin masu burin shiga zaben na APC a Katsina.

en_USEnglish
en_USEnglish