AMURKA ZATA KAKABAWA IRAN TAKUNKUNMIN TATTALIN ARZIKI.

Kasar amurka ta gabatar da sababbin sharadai 12 masu tsauri domin kulla yarjejeniyar nukiliyar iran, lokacin da kasar ta yi barazanar daukar matakai masu tsauri kan kamfanonin kasahen turai da suka cigaba da hulda da ita.

Yayin da yake gabatar da sabbin manufofin amurka kan kasar iran, sakataren harkokin waje mike pompeo ya ce zasu kakabawa iran takunkumin karya tattalin arzikin mai karfin da ba su taba yi ba a tarihi, bayan janye kasar daga yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015.

Pampeo ya ce manufofin amurka na farko tun bayan nadin da aka masa,amurka zata tabbatar da dakile karfin fada ajin iran da ke fadadawa a gabas ta tsakiya da kuma gindaya sharidodi 12 masu tsauri domin kulla wata sabuwar yarjejeniya.

Sakataren harkokin wajen yace matakan da za su dauka zai nunawa shugabannin iran cewar da gaske su ke wajen bayyana kudirorin su kan kasar.

Tuni dai kasashen turai suka bijirewa amurka wajen kin bin umarnin ta wajen harka da iran da kuma sanya dokar da zata kare kamfanonin su dake harkokin kasuwanci a iran.

en_USEnglish
en_USEnglish