KASAR KONGO TA FARA BADA RIGAKAFIN KARIYA DAGA CUTAR EBOLA.

Jami’an lafiya a jamhuriyyar dimokaradiyyar congo sun fara gudanar da aikin baiwa jama’a rigakafin cutar ebola, a wani yunkurin da ake na dakile yaduwar cutar zuwa wasu sassan kasar.

Cutar ebola dai na cigaba da yaduwa a kasar congo duk da matakan da hukumomin ke dauka na ganin sun kawar da ita.

Tun da fari dai an taba amfani da maganin rigakafin a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016, kuma an samu nasara a wancan lokacin.

Fara aikin rigakafin ya zo a dai-dai lokacin da ma’aikatar lafiyar kasar ta sanar da karuwar wadanda suka hallaka a dalilin kamuwa da cutar zuwa 26 bayan mutuwar wata jami’ar jiyya.

Tuni dai kasashen nahiyar afrika suka fara daura damarar ganin sun kare al`ummarsu daga cutar ta Ebola mai hadarin gaske.

en_USEnglish
en_USEnglish