KUNGIYAR LAUYOYI JUSUN TA SHIGAR DA GWAMNATIN JIHAR KANO KARA.

Babbar kotun jiha mai lamba 9 karkashin mai shari’a Usman Na’Abba taci gaba da saurarar karar da kungiyar ma’aikatan shari’a “JUSUN” suka shigar suna karar gwamnatin jihar kano dangane da batun neman takardun biyan albashi da gwamnatin jihar kanon ta nemi sashin shari’ar su gabatar.
Kungiyar jusun dai ta garzaya kotun domin jin ko gwamnatin jihar tana da hurumin karbar takardun jawabin albashin su sai dai kotun ta sanya ranar19 ga watan gobe dan ci gaba da shari’ar wakilinmu yusuf Nadabo ismail ya zanta da mataimakin shugaban kungiyar Zaharaddin Abdu Fagge wanda yayi karin haske.

en_USEnglish
en_USEnglish