RUNDUNAR YAN SANDAN JIHAR KANO TAYI GARGADI GA IYAYE.

Rundunar Yansandan Jihar Kano ta gargadi Iyaye su ja kunnen Yayansu Kan amfani da abun fashewa mai kara wato Nockout Musamman lokacin watan Azumin Ramadan.

Kakakin rundunar a nan Kano SP Magaji Musa Majiya ne. Ya bayyana hakan a zantawarsa da gidan Rediyon Dala kan yadda kananan yara ke amfani da Nockout wajen razana al`umma musamman a lokacin Ibada.

SP Magaji Musa Majiya, ya kara da cewar lokaci ya wuce da iyaye zasu zuba idanu kan Yayansu nayin abubuwan da basu kamata ba

SP Magaji Musa Majiya, ya kuma ce akwai bukatar al`umma su dauki matakin gyara tarbiyar yayansu da na makota maimakon zuramusu idanu.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewa rundunar Yansandan Jihar Kano ta kuma nemi hadin kan a’lumma wajen cigaba da gudanar da aikin su na kare rayuka da dukiyar al’umma.

en_USEnglish
en_USEnglish