KOTUN TARAYYA TA BAYAR DA BELIN TSOHON GWAMNAN KANO MALAM IBRAHIM SHEKARAU, AMBASADA AMINU WALI DA ENGINEE MANSUR AHMAD.

Babbar kotun tarayya mai zaman ta a kano karkashin justice zainab abubakar ta fara saurar karar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta shigar gabanta tana karar tsohon gwamnan jihar kano Malam Ibrahim Shekarau da kuma tsohon ministan harkokin waje ambasada Aminu Wali da kuma tsohon kwamishinan ayyuka a kano Eng. Mansur Ahmed bisa zargin hada baki da yin badakala ta naira miliyan 950.

Hukumar EFCC ta yi zarginsu ne da karbo kudin a hannun jam’iyyar PDP a ranar 27 ga watan Maris 2015 inda suka rabe kudin a gidan tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau kamar yadda zargin ya nuna.

Sai dai dukkanninsu sun musanta zargin inda lauyoyin da ke karesu da suka hada da Barr Faruk Sambo iya, da Barr Abdul Adamu Fage da Barr Abdulkarim Maude Minjibir suka roki kotun data sanya su a hannun beli.

Sai dai lauyan hukumar Barr Johnson Ojubame ya soki lamirin.

Wakilin mu na kotu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa kotun ta sanya su a hannun Beli bisa sharadin kawo ma’aikatan gwamnatin biyu ga kowanne kuma wadanda suka kai matsayin darakta a matakin jiha ko tarayya da kuma hotunansu. Idan kuma wadanda ake zargi suka tsere wadanda suka amshe su beli za su biya naira miliyan dari kowane.

Mai sharia Zainab Abubakar ta sanya ranar 26 ga watan gobe domin cigaba da saurar shari’ar.

Jim kadan da fitowa daga shari’ar ne wakilinmu Yusuf Nadabo ya tattauna da lauyan wadanda ake tuhuma Barr. Abdul Adamu Fage

en_USEnglish
en_USEnglish