KWAMISHINIYAR MA’AIKATAR ALBARKATUN KASA TA JIHAR ADAMAWA TA RASA WASU DAGA CIKIN HAKORANTA SAKAMAKON MARI DA TA SHA.

Kwamishiniyar ma’aikatar albarkatun kasa ta jihar Adamawa Misis Shanti Sashi, ta maka shugaban karamar hukumar Lamurde Mista Barati Nzonzo a kotu, biyo bayan marin da ya wanka mata wanda ya yi sanadiyar cire mata hakori.

Misis Sashi, ta maka shugaban karamar hukumar ne a kotu kan batutuwa bakwai da suka shafi aikata munanan laifuka, ta kuma zargi shugaban da ci mata mutunci da azaba mai tsanani, da ya kai ta ga rasa hakoranta.

Sai dai lokacin da aka kira shari’ar gaban wata kotun majistare a ranar juma’ar da ta gabata a Yola, wanda ake zargin bai sami halartar zaman kotun ba .

Lauyan dake kare wacce ta kara, Misis Mfoniso Gabriel, ta bukaci kotun da ta yi amfani da sashi na 154 karamin sashi na 1, na kundin tsarin dokar masu aikata miyagun ayyuka (CPC) ta bada umurnin kamo wanda ake zargin.

Shi kuwa Mista Jerry Ifegwu, lauyan da ke kare wanda ake zargin ya ce, batun amfani da waccan dokar bai taso ba, domin wanda yake karewa bai bayyana a kotun ba. Ya ce duk da wanda yake karewa bai bayyana a kuton ba, amma ya samu labarin wasu manoma sun kai hari kan wasu kauyuka a karamar hukumar Lamurde, lamarin da ya tilasta mishi tafiya yankin a matsayinsa na babban jami’in tsaro a yankin.

Yanzu haka dai mai sharia Momsiri Bamare, ta dage sauraron shari’ar zuwa 25/5/2018, domin ci gaba da sauraron karar.

en_USEnglish
en_USEnglish