MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR BAUCHI YA RUBUTA TAKARDAR BARIN AIKI GA GWAMNAN JIHAR.

Mataimakin gwamnan jihar Bauchi Injiniya Nuhu Gidado,ya mikawa gwamnan jihar bauchi Muhammad abubakar takardar ajiye aiki.

A cikin wasikar da ya mika ya bayyana dalilansa, inda yace dama bashi da niyyar wuce wa`adin mulki daya akan wannan mukamin.

Sai dai gwamnan jihar Muhammad abubakar ya ce ya dauki mataimakin nasa da muhimmancin gaske a gwamnatinsa, kuma ko anan gaba ana iya nemansa ya taka wata rawa nan gaba.

Tun a ranar 16 ga watan da muke ciki ne mataimakin gwamnan ya rubuta wasikar ga gwamnan, inda ya nuna sha’awarsa ta yin murabus daga matsayinsa, inda yace ya yi hakan ne a bisa yanke shawara da ya yi cewa wa’adin mulki daya kawai yake so ya yi a matsayin mataimakin gwamna.

Ya kara da cewa yakamata ace ya jira a karasa wa’adin mulkin nan da shi, amma ba zai samu damar tsayawa a karasa dashi ba, saboda wasu dalilai na shi na kashin kansa.

A karshe ya mika godiyar shi ga gwamnan jihar Bauchi da ilahirin mutanen Bauchi bisa abinda ya ce goyon bayan da suka bashi har ya zama mataimakin gwamnan a jihar .

 

en_USEnglish
en_USEnglish