SHUGABAN MUHAMMADU BUHARI YAYI ALLAH WADARAI DA YANDA AKE HALLAKA YAN KASA.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da hallaka rayukan ‘yan kasa da ake samu da sunan fada tsakanin manoma da makiyaya a wasu sassan kasar nan.

Yace gwamnatin san a daukar matakan da suka dace domin ganin an gurfanar da dukkanin masu hannu akan wannan al’amari a gaban kuliya.

Shugaba Buhari na wadannan kalamai ne a jawabin daya gabatar yau da safe, domin murnar cikar najeriya shekaru 19 akan tafarkin demokaradiyya babu katsewa.

Haka zalika bikin na yayi dai-dai da cikar gwamnatin shugaba Buihari shekaru uku akan karaga.

Shugaban kasar yace tuni aka baiwa jami’an tsaro umarnin farautar masu kitsa fitina da sunan fada makiyaya da manoma musamman a jihohin Taraba da Benue da sauran jihohi dake fuskantar matsalar tsaro.

Shugaban kasar yace dukkan fallen gwamnati uku na kasar nan na aiki tare da shugabannin addini dana al’uma da kuma sarakunan gargajiya domin wanzar da zaman lafiya a kasa baki daya.

en_USEnglish
en_USEnglish