YAU NE NAJERIYA KE CIKA SHEKARU 19 A TAFARKIN DEMOKARADOYYA.

 

Yau ranar demokaradiyya a najeriya kuma tuni gwamnatin tarayya ta kebe wannan rana a matsayin hutu ga ma’aikatan gwamnati dana cibiyoyi masu zaman kansu.

A ranar 29 ga watan nan na Mayu ne a shekarar 1999 najeriya ta koma tafarkin demokaradiya kuma tun daga wancan lokaci ake ci gaba da mulkin demokaradiyyar babu kastsewa.

Gwamnatoci a matakai daban daban na amfani da wannan rana domin gabatar da jawabai kan nasarorin da suka samu wajen samar da ribar demokaradiyya ga ‘yan kasa.

Haka zalika, akan gudanar da tarukan lacca game da riba da kalubalen da wannan demokaradiyya ta najeriya ta samar ga talakan kasa, inda masana a fannoni daban daban keyin fashin baki da kuma wayar da kan jama’a game da salon mulkin demokaradiyya.

Dangane da wannan rana ce wakilinmu Muazu Musa Ibrahim ya tattara mana ra’ayoyin ‘yan najeriya a nan Kano dangane da shafe shekaru 19 a kasar nan ana gudanar da demokaradiyya babu katsewa.

 

en_USEnglish
en_USEnglish