ANYI KIRA GA YAN SIYASAR KASAR NIJAR.

Kungiyoyin kare hakkin bil’ada sun yi jan hankali ga ‘yan siyasar kasar Nijar da su sasanta da juna domin kaucewa jefa kasar cikin rudanin siyasa

 

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na nuni da cewa Ja-in-ja tsakanin yan ‘yan siyasa tayi ‘kamari, game da manyan zabukan kasar masu gabatowa

Matakin daya tilastawa kungiyoyin kare hakkin jama’a fara jawo hankalin yan siyasar da su zauna teburin sulhu ta yadda za’a shirya zabukan cikin lumana.

Dambarwar ta biyo bayan kallo da yan adawa ke yiwa gwamnatin Nijar na kin amincewa da bukatar sauyi kan hukumar zabe, lamarin da kungiyoyin kare hakki anasu bangaren ke ganin hukumar zaben ka iya taka muhimmiyar rawa wajen zama da ‘yan adawar domin basu tabbacin aiwatar da zabe mai tsafta

Ita dai hukumar zaben da aka kafa bayan an yiwa kundun tsarin zabe kwaskwarima hukuma ce da ‘yan adawa ke yiwa kallon ‘yar amshin shata, lamarin da ya hanasu aikewa da wakilci zuwa cikin ta.

 

en_USEnglish
en_USEnglish