GWAMNATIN JIHAR FILATO TA SAMAR DA DANDAMALIN TATTARO BAYANAI

Gwamnatin jihar Filato ta samar da wani dandamalin tattaro bayanai domin inganta harkokin tsaro a fadin jihar

Da yake kaddamar da dandamalin, Gwamna Simon Bako Lalong yace manufar hakan tana da nasaba da kokarin su na tabbatar da cikakken tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, kamar yadda suka alkawarta

Gwamnatin jihar Filato ta ce ta samar da motoci da kayan aiki na zamani da zai taimakawa dandamalin mai suna Operation Rainbow, wajen samar da bayanan neman ‘dauki cikin gaggawa a duk inda aka samu matsalar tsaro a fadin jihar.

Gwamna Lalong yace daukan wannan mataki ya zama dole saboda matsalolin tsaro da a ke samu jifa-jifa a wasu sassan jihar. Yace sun rabawa sojoji da jami’an tsaro motoci na musamman da zasu gano matsaloli na tsaro a ko yunkuri na tashin hankali a sassan jihar

 

 

en_USEnglish
en_USEnglish