HUKUMAR INEC TASHA ALWASHIN TABBATAR DA ZABE MAI INGANCI A SHEKARAR 2019.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC tasha alwashin tabbatar da zabe mai inganci a zaben badi.

Mai magana da yawun hukumar, Malam Aliyu Bello, ya shaidawa manema labarai cewa, zaben 2019 sai yafi na 2015 inganci da nagarta da kuma dukkan matakan da ya kamata abi.

Malam Aliyu, ya ce a zaben 2019, ba wanda zai kai ga nasara sai wanda jama’a ta zaba, sai kuma wanda goyon bayansa ya bayyana wato wanda kuri’a ta zaba.

Mai magana da yawun hukumar zaben ya ce, ‘ Tanadin hukumar zabe a kullum shi ne a tabbatar da sahihin zabe a 2019’.

Malam Aliyu Bello ya ce, daga cikin matakan tabbatar da sahihin zabe a 2019, shi ne fara bayar da rijistar zabe ga wadanda suke basu da ita, ko kuma wadanda suke da ta wucin gadi.

 

 

en_USEnglish
en_USEnglish