TSOHON SHUGABAN HUKUMAR ZABE YA BAYYANA MATSAYARSA GAME DA ZABEN 2019.

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ‘INEC’, Farfesa Attahiru Jega ya yi shelar cewa babban zaben shekarar 2019 mai gabatowa ka iya fuskantar tarnaki.

Farfesan ya bayyana matsalolin da aka yi ta samu a zaben cikin gidan jam’iyyar APC, da kuma zargin badakalar cin hanci a Majalisar tarayya a matsayin wasu ababe da za su iya kawo wa zaben cikas.

Jega ya bayyana matsayar tasa ne a yayin da yake gabatar da jawabin ranar dimokradiyya a Abuja, taron da ya samu halartar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, da Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara da wasu manyan kasa.

Tsohon Shugaban na INEC ya yi gargadin cewa samun rikice-rikice a zaben cikin gidan jam’iyyar APC na iya zama barazana. Inda ya ce, matukar uwar jam’iyyar ba ta iya yin zaben cikin gidanta lafiya, to me za a tsammata daga babban zabe?

Haka kuma ya kara kafa hujja da karuwar annobar kalaman batanci a tsakanin al’umma, wanda ya ce dole ne a tashi tsaye domin kawo karshensa, idan kuwa ba haka zaben zai fuskanci matsala.

 

en_USEnglish
en_USEnglish