MAJALISAR DATTAWAN NAJERIYA TAYI SAMMACIN KWANTROLAN GIDAJEN YARI

Majalisar dattawa tayi sammacin kwantrolan gidajen yari na kasa ,ahmed ja`afaru domin yi mata bayani kan yadda ake samun rahoton garkame kananan yara a gidajen yari.

Dan majalisa mai wakiltar anambra sanata victo umeh ne ya ja hankalin majalisar kan rahotanni da jaridun kasar nan ke yadawa kan garkame kananan yara da suka aikata ba dai-dai ba.

Victo umeh ya bayyana karbuwa da ganin hotunan kananan yara yan kasa da shekaru goma sha biyar,a wasu gidajen yarin kasar nan da aka ware domin daure manyan masu aikta laifuka.

 

 

en_USEnglish
en_USEnglish