MASU RUWA DA TSAKI AKAN HARKOKIN AIKIN HAJJI NA CIGABA DA KOKAWA GAME DA FARASHIN KUDIN AIKIN HAJJIN BANA.

Masu ruwa da tsaki akan harkokin aikin hajji a kasar nan na cigaba da kokawa bayan da hukumar alhazai ta ayyana kudin kujerar hajjin bana wato shekarar 2018.

kamar yadda akayi a shekarar da ta gabata na 2017 kowacce jihar na da nata farashin kujerar,sai dai a wannan karan an sami saukin kujerar zuwa hajjin bana idan aka kwatanta da shekarar bara.

A bana kudin kujerar naira million daya da dubu dari hudu da sittin da biyar da dari biyar(1,465,500) na ko wani alhajin jihar neja zai biya, inda aka sami ragin naira dubu hamsin da daya da dari biyar(51,500).

Shugaban kungiyar izala na kasar nan Sheik Abdullahi Bala Lau. Ya ce saukin bai isa ba, a don haka ne yayi kira ga hukumar Alhazai data kara dubawa domin sake samun sassauci.

Sakataren hukumar Alhazan   jihar neja Shehu Barwa Beji ,ya bayyana dalilin da ya sa aka samu rangwami. Ya ce gwamnan jihar Neja ya amince da dauke biyan kudin jakunkuna,a cewarsa gwamnati ce zata biya.

Hukumar jin dadin Alhazan jihar ta ce ta dauki matakin dakile duk wata cuwa-cuwar damfarar maniyyata kamar yadda wani jami`in hukumar Umar Maku Lapai ya shaida . ya kara da cewa babu wani ma`aikacin hukumar da aka bawa izinin ya karbi kudi daga hannun wani Alhaji. ma`aikatar karamar hukuma ce ke da wannan hakkin.idan kuma har aka sami wani ma`aikaci da yin hakan to zai fuskanci fushin hukuma.

Haka zalika jihar neja ta samu daya daga cikin na`urorin da hukumar alhazai ta kasa ta raba domin gudanar da tantace lafiyar alhazan kamar yadda hukumomin kasar saudiyya suka nemi ayi.

en_USEnglish
en_USEnglish