HUKUMAR LAFIYA TA DUNIYA TA FARA GANGAMIN KAWAR DA CUTAR SHAWARA A NAJERIYA.

Hukumar lafiya ta duniya tace ta fara gangamin kawar da zazzabin Yellow fever a najeriya tun daga watan Fabarerun bana.

Hukumar tace ta raba sinadarin rigakafin cutar ga mutane miliyan 2 a sansanin ‘yan gudun hijira daban daban a jihar Borno da kuma sauran kauyuka na jihar.

Jami’ar sadarwa ta hukumar lafiyar a nan najeriya Madam Charity Warigon ta ambata haka cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a can Abuja.

Tace za’a ci gaba da gudanar da gangamin zuwa karshen wannan shekara, inda ake sa ran bada riga kafin ga mutane miliyan 25 a sassa daban daban na kasar nan.

Madam Charity ta yi bayanin cewa, matakin ya biyo bayan rahotan samun bullar cutar ne tun a bara, inda aka tabbatar da samunta a jihar Kwara.

en_USEnglish
en_USEnglish