KUNGIYAR KARE HAKKIN ZABIYA TA KASA TA KOKA GAME DA YANDA AKE NUNA MUSU WARIYAR LAUNI.

Kungiyar kare hakkin zabiya ta kasa ta koka kan yadda ake nunawa zabiya wariyar launin fata da al’umma ke nuna masu.

Kungiyar ta bayyana hakan ne yayin wani taron ‘ya’yan kungiyar zabiya da ta shirya a birnin tarayyar Abuja.

Ta ce akwai bukatar al’uma su gane cewa babu wata illa don A… ya baiwa mutum rabo na da ko diya zabiya a kyamace shi, domin kuwa suma mutane ne kamar kowa.

Da yake jawabi yayin taron, babban alkalin kotun birnin trayyar Abuja, Mai Shari’a Usman Bello, ya bayyana takaicin jin yadda ake nunawa zabiya wariyar launin fata.

Yace irin wannan taro yana da muhaimmanci wajen kara wayarda kan al’uma kan bukatar su kara gyara halayen su na wajen daina tsangwama da danne hakkin zabiyan a wuraren daukar aiki da sauran mu’amalolin yau da kulum.

Kungiyar ta ce ko a kwannan ma daya daga cikin su, yaje aikin horo na shiga aikin Dansanda, kuma ya nuna bajinta, amma daga bisani aka ki bashi takardar kama aiki.

en_USEnglish
en_USEnglish