HUKUMAR KULA DA BININ ABUJA TA ANKARAR DA MAZAUNA BIRNIN KAN YUWUWAR AMBALIYA A DAMINAR BANA

Hukumar kula da birnin tarayya Abuja ta ankarar da mazauna birnin game da yuwuwar samun ambaliyar ruwa a sassan birnin da kewaye a daminar bana.

Haka kuma hukumar tayi kira ga mazauna Abuja da kewaye su guji gini ko kafa rumfuna ba bisa ka’aida ba kana da kuma zuba shara a magudanan ruwa.

Wadannan kalaman sun fito ne daga bakin Ministan Abuja Malam Musa Bello yayin ziyarar jaje ga mutanen garin Karshi na yankin Abuja biyo bayan annobar ambaliyar ruwa data wakana a garin a shekaranjiya asabar.

Haka kuma ministan ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su sakamakon ambaliyar ruwa a kauyen Kokosu na jihar Nasarawa wadda ke makwaftaka da yankin Karshi.

Rahotanni sunce mutane biyu ne suka mutu a kauyen na Kokosu sanadiyyar mamakon ruwan sama wanda ya haifar da ambaliyar ruwa a yankin.

Ministan wanda babban sakatare a ma’aikatar kula da birnin tarayya Abuja Sir Chinyeaka Ohaa ya wakilta ya yi amfani da ziyara domin tantance irin barnar da ambaliyar tayi.

en_USEnglish
en_USEnglish