MAIDAKIN SHUGABAN KASA AISHA BUHARI TAYI JAN HANKALI GA MATA.

Mai dakin shugaban kasa Hajiya A’isha Buhari ta yi kira ga mata su kasance a sahun gaba wajen kira ga batutuwan wanzar da zaman lafiya a tsakanin matasan najeriya.

Madam Buhari tace hadin kan najeriya da zaman lafiya tsakanin al’umarta ba abin wasa ba ne.

Mai dakin shugaban kasar na wadannan kalamai yayin bude baki da wasu shugabannin mata a fadar gwamnati dake Abuja a karshen mako.

Tace shan ruwa da abokai a lokacin azumin ramadana na kara dankon zumunci da hadin kai al’umma.

Hajiya Aisha Buhari ta tunasar da iyaye mata bukatar dake akwai agaresu mata su wajen daukar matakan da suka kamata domin kubutar da ‘yayan su daga fadawa hannun bata gari dake amfani dasu wajen aikata miyagun ayyuka.

A nata jawabin, mai dakin mataimakin shugaban kasa Madam Dolapo Osinbajo ta bukaci ‘yan najeriya su rinka sanya tsoron Allah a dukkanin al’amuran su na yau da kullum.

Tace mata nada muhimmiyar rawar takawa dakile fitintinu a tsakanin al’umma.

en_USEnglish
en_USEnglish