WASU FURSUNONI SUN TSERE DAGA GIDAN KURKUKU NA GARIN MINNA.

Hukumar kula da gidajen yari ta kasa ta tabbatar da cewa, wasu daurarru sun tsare daga gidan kurkuku na garin Minna a jihar Neja a jiya lahadi.

Kodayake hukumar ba ta ayyana adadin fursunonin da suka balle kuma suka fice gidan yarin na Minna ba, amma kakakin hukumar a jihar Niger Rabiu Shu’aibu yace jami’an hukumar sun sake kamo 7 daga cikin su.

Sai dai yace guda daga cikin jami’an hukumar ya rasa ransa a yayin farmakin balle gidan kurkukun na Minna.

Malam Rabiu Shu’aibu ya yi bayanin cewa, wasu tsageru ne suka fara kai farmaki akan gidan yarin da nufin shiga ciki kuma a yayin musayar wuta da Gandirebobin dake bakin aiki guda cikin ya rasa ransa.

Yanzu haka dai hukumomin kula da gidan yarin na Minna na na sake nazarin alkaluman daurarrun dake ciki domin tantance adadin fursunonin da suka tsare.

A sanarwar da kakakin gidan Yarin Malam Rabiu Shu’aibu ya fitar tace ya zuwa yanzu al’amura sun dai-daita a harabar kurkukun kuma jami’ai na aiki tukuru domin dawo da ragowar daurarrun da suka tsare.

en_USEnglish
en_USEnglish