YAU MA’AIKATAN LAFIYA DA BA LIKITOCI BA SUKA KOMA AIKI BAYAN SHAFE FIYE DA KWANAKI 40 SUNA YAJIN AIKI.

Yau mambobin kungiyar ma’akatan lafiya ta kasa wadanda ba likitoci suka koma bakin aiki bayan shafe kwanaki 45 suna yajin aiki.

Tun a cikin watan Afrilun bana ne uwar kungiyar ta kasa ta umarci ‘yayanta su kauracewa wuraren ayyukan su saboda takaddamar da ke tsakanin su da gwamnatin tarayya.

Takaddamar ta biyo bayan abin da kungiyar ta kira rashin mutunta yarjejeniyar da suka cimma da gwamnati game da wasu bukatun kungiyar.

Bukatun sun hada da dai-daita al’amura kan sha’anin albashi da dangodin sad a batun samar da kayayyakin aiki a daukacin asibitoci da ciboyoyin shan magani dake fadin najeriya kana kuma tabbatar da adalci wajen tsarin shugabancin hukumomin kiwon lafiya na sassan kasar nan.

Yajin aikin na tsawon kwanaki 45 ya sanya ayyukan lafiya sun durkushe a fadin kasar nan, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane masu yawa yayin da marasa lafiya da dama suka kara galabaita.

en_USEnglish
en_USEnglish