AN KAFA KWAMIITIN BINCIKE GAME DA HARIN DA AKA KAI GIDAN YARIN JIHAR NAIJA.

Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin bincike kan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai sabon gidan yarin Minna, a jihar Neja ranar Lahadin da ta gabata.

Ministan harkokin cikin gida, Janar Abdulrahaman Dambazzau mai ritaya ne, ya sanar da haka, yayinda ya jagoranci wata tawagar da ta kai ziyarar gani da ido gidan yarin a jiya Litinin.

Yace tawagar ta je Minna ne domin duba abun da ya faru da nufin daukar matakan kaucewa sake aukuwar hakan anan gaba.

Yace ziyarar zata ba su damar sanin inda suka yi kuskure da kana kuma su koyi darasi daga faruwar al’amarin.

Janar Dambazzau ya kara da cewa fursinoni 210 ne suka gudu a lokacin harin, inda ake fatan nan da ‘yan kwanaki za’a dawo dasu.

Yace Kawo yanzu jami’ai sami nasarar dawo da 30 daga cikin fursunonin da suka tsare.

Gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya yi alkawarin bada gudummawar da ta dace domin kara tsaurara tsaro a gidan yarin na Minna.

 

en_USEnglish
en_USEnglish