FIYE DA DALIBAI HAMSIN NE SUKA KAMU DA CUTAR KWALARA.

Fiye da dalibai hamsin ne suka kamu da cutar kwalara tare da hallaka wasu guda biyu a safiyar jiya litinin a makarantar ‘yan mata ta GGSS dake Kawo a jihar Kaduna.

Kwamishinan ilimi na jihar Kaduna, Alhaji jafaru sani ya tabbatar da hakan ga manema labarai, inda yace binciken da aka gudanar an samu dalibai kimanin 55 da suka kamu da cutar.

kwamishinan ya kara da cewa an sami bullar cutar ne sakamakon karancin wutar lantarki da ruwan sha da sauran kayan amfanin makarantar.

Alhaji Jafaru yace an shafe kwana uku babu hasken lantarki a makarantar.

Tuni dai aka garzaya da daliban da suka kamu da cutar zuwa babban asibitin jihar kaduna domin basu agajin gaggawa.

 

en_USEnglish
en_USEnglish