WASU DAGA CIKIN KUSOSHIN JAM’IYYAR APC SUNCE AN MAYAR DASU SANIYAR WARE.

Wasu kusoshin Jam’iyyar APC dake korafin cewa, an mayar da su saniyar ware a harkokin gwamnati da na Jam’iyya sunce ba zasu sake wani zaman tattaunawa da fadar shugaban kasa ba.

Ayarin jagororin na APC karkashin shugabancin Alhaji Kawu Baraje sun hada da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara da sanata Rabiu Kwankwaso da sauran tsaffin ‘yayan Jam’iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa APC a shekara ta 2014.

A kasarshen mako ne da sukayi wata ganawa da maitaimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a wani mataki na waware takaddamar dake tsakanin su da gwamnati da kuma Jam’iyya.

Sai dai a wata sanar da shugaban ayarin Alhaji Kawu Baraje ya fitar a Abuja, yace sun dauki matakin kauracewa ci gaba da tattaunawa da fadar shugaban kasa ne la’akari da yadda gwamnati ke amfani da wasu kafofin ta domin muzguna musu.

Yace janye jami’an tsaron dake bada kariya ga shugaban majalisar dattawa nada wakilai na nuna cewa gwamnati ta daina sha’awar zaman sasantawa game da lamarin.

Baya ga haka, inji Alhaji Kawu Baraje shugabancin jam’iyyar APC ya ci gaba da amincewa da sakamakon zaben shugabannin jam’iyya a matakan mazabu da kananan hukumomi da kuma na jihohi duk kuwa da korafin da suka mika game da yadda zabukan suka wakana.

Alhaji Kawu Baraje ya yi bayanin cewa, ba zasu iya ci gaba da zaman sulhu ba a yayin da gwamnati ke amfani da hukumomin tsaro tana muzgunawa mambobin sa ba.

en_USEnglish
en_USEnglish