KOTU TA BAYAR DA BELIN TSOHON GWAMNAN JIHAR KADUNA DA WASU MUTANE UKU.

Babbar kotun tarayya dake zamanta a Kaduna ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero da wasu mutane uku

Tunda farko lauyan masu kariya Barista Yunus Ustaz ne ya roki mai sharia Justice Muhd Shuaib ya bashi belin wadanda yake karewa, bukatar da lawyan masu korafi Barrister Joshua Saidi yayi suka akai.

Bayan takaddama tsakanin bangarorin biyu a karshe mai shari’a Muhd Shuaib ya bayar da belin Ramalan Yero da sauran mutane 3 akan kudi naira miliyan guda kowannen su, da kuma mutane biyu da zai tsaya musu. Haka kuma kotun ta nemi wadanda ake tuhumar su ajiye fasfunan su a hannun maga takardar kotun, inda ta dage cigaba da sauraron karar zuwa 26 ga watan satumba

Tun a makon daya gabata ne dai kotun ta bayar da umarnin a cigaba da tsare wadanda ake zargin zuwa yau, bisa tuhumar su da kaucewa ka’idar dokar kasa kan mallakar kudade da kuma fidda su ba bisa ka’ida ba lokacin suna jagorancin jihar kaduna

Wadanda aka bayar da belinnasu sun hadar da tsohon shugaban jam iyyar PDP na kaduna Abubakar Gaya-Haruna, tsohon sakataren gwamnati Hamza Ishaq da tsohon ministan lantarki Nuhu Somo Way da kuma tsohon gwamnan kaduna Ramalan yero.

 

en_USEnglish
en_USEnglish