WASU MAZAUNA GARIN OFFA SUN GUDANAR DA ZANGA-ZANGAR NUNA ADAWA KAN GORON GAYYATAR DA RUNDUNAR YAN SANDA TA TURAWA BOKOLA SARAKI.

Wasu mazauna garin Offa dake jihar kwara sun gudanar da wata zanga zangar nuna adawa da matakin rundunar yan sandan kasarnan akan goron gayyatar da ta aikewa shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki

A ranar lahadin data gabata ne rundunar yan sandan kasarnan ta aikewa Sanata Bukola Saraki sammacin bayyana gaban ta, domin amsa tambayoyi.

Rundunar yan sanda a jihar kwara na bincike ne kan wadansu mutane 5 da aka kama bisa laifin fashi da makami, inda cikin jawabansu suka ambato sunan Sanata Bukola Saraki, alamarin daya haifar da zangar zangar lumana a jihar kwara

Ko a ranar litinin data gabata sai da wasu mazauna jihar suka gudanar da zanga zangar nuna goyon baya ga hukumar yan sanda, kan goron gayyatar data aikewa sanatan a farkon wannan mako.

en_USEnglish
en_USEnglish