TSOHON BABBAN JOJIN KASAR NAN YA CE BAYAR DA LAMBAR YABO MAFI GIRMA GA MKO ABIOLA YA SABAWA DOKA.

Tsohon babban jojin Nigeria mai shari,a Alfa Belgore ya ce bayar da lambar yabo mafi girma a Nigeria ta GCFR ga marigayi MKO Abiola baya bisa tafarkin doka.

Da yake zantawa ga manema labarai Alfa Belgore a Abuja ya ce baya bisa tsarin doka a bayar da irin wannan lamba ta karramawa mafi girma ga mutumin da ya riga ya mutu.

Ya ce dokar kasa ta kebe irin wannan lamabar yabo ne ga mutanen da suke raye kadai.

Mai shari’a Alfa Belgore wanda ya rike kujerar baban jojin kasar nan daga shekara ta 2006 zuwa 2007 ya ce abin da shugaba Buhari ya kamata yayi domin girmama Marigayi MKO Abiola shi ne ya sanya sunansa a wasu muhimman gurare na kasar nan.

Ya ce dokar bada da lambar yabo ta kasa ta shekarar 1963 ta ce za a iya bada irin wannan lambar yabo ga mutanen da suka mutu amma ga sojojin da suka mutu fagen fama ko kuma sauran jami’ai masu sanye da kayan sarki.

Mai Shari’a Alfa Belgore wanda shi ne shugaban kwamitin bayar da lambobin yabo na kasa a shekara ta 2016 ya ce shugaba Buhari bai tuntube shi ba gabanin ya yanke hukuncin bada wannan lamba ta GCFR ga Marigayi Abiola.

 

en_USEnglish
en_USEnglish