KASAR AMURKA TA TABBATAR DA CEWA BA ZATA JANYE KUDIRINTA NA SANYAWA WASU KASASHE HARAJI BA.

Mai ba shugaban Amurka shawara akan harkokin tattalin arziki ya tabbatar cewa shugaban zai tsaya kan harajin da ya kakaba wa wasu kasashe da suka fi karfin masana’antu ataron G7.

Daya daga cikin manyan masu baiwa shugaban Amurka shawara akan tattalin arziki Larry Kudlow ya fadawa yan jarida jiya Laraba cewa shugaba Donald Trump na Amurka zai tsaya akan bakarsa wajen taron kolin kungiyar kasashe masu arzikin masa’antu da ake cewa G7 a takaice, da za’a yi duk da caccakar manufofi harkokin kasuwancin Amurka da kawayen Amurka suka ke suke yi.

 

Mr Kudlow yace galibi akan samu sabanin ra’ayi tsakanin Amurka da sauran kasashe wakilan kungiyar G7. Ya kuma musunta cewa Amurka tana rikici akan harkokin cinnikaya da kawayen ta da kuma China, amma yace Amurka zata dauki duk matakan da suka kamata na kare ma’aikatan Amurka da masana’antunta.

 

 

 

 

en_USEnglish
en_USEnglish