RUNDUNAR YAN SANDAR KASAR NAN TA CE LALLAI NE SAI SHUGABAN MAJALISAR DATTAWA YA BAYYANA GABANTA..

Rundunar yan sandar kasar nan ta bayyana cewa dole ne shugaban majalisar dattawa sanata Bukola Saraki ya bayyana gabanta domin ya amsa wasu tambayoyi kan zarginsa da take kan sunansa da yan fashin da aka kama a fashin yankin OFFA suka bayyana.

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da wasu yan fashin da aka kama suka sake bayyana sunansa a matsayin mutumin da suke da alaka da shi.

Tun bayan da Yan fashin suka bayyana sunan sanata Sarakai ne wasu rahotanni suka bayyana cewa rundunar yan sanda ta nemi Saraki ya amsa tambayoyin da za su yi masa a rubuce ya kuma mika mata batun da mai magana da yawun rundunar yan sandar ACP Jimoh Mashood ya musanta.

ACP Jimoh ya ce binciken da suka sake yi ya nuna musu cewa wadanda ake zargi a kan fashi da makamin da suka hada da Ayoade Akinnibosun, Ibukunle Ogunleye, Adeola Abraham sun yi rakiya ga shugaban majalisar zuwa fadar Oloffa domin yin ta’aziyya bayan faruwar fashin.

 

en_USEnglish
en_USEnglish