SHUGABAN KASA MUHAMMAD BUHARI YA BAYAR DA LAMABAR YABO MAFI GIRMA GA MARIGAYI MKO ABIOLA.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauya ranar bikin tunawa da Dimokradiya daga 29 na watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni domin tunawa da Chief MK O Abiola wanda aka yi ikirarin shi ya lashe zaben shugaban kasa na wannan shekarar kafin gwamnatin IBB ta soke zaben

Tuni dai al’ummar kudu maso yammacin Najeriya suka yi maraba da sauya ranar bikin Dimokradiyar zuwa 12 ga watan Yuni maimakon 29 na watan Mayu domin tunawa da gwagwarmayar tsohon dan kasuwar kuma dan siyasa Chief Moshood Abiola.

Chief Abiola dai shi ake ikirarin ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993. Amma gwamnatin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta lokacin ta soke.

A martanin da ta fitar gwamnatin jihar Lagos ta yaba da matakin da shugaba Muhammad Buhari ya dauka a matsayin tukwicin da al’ummar kudu maso yammacin Najeriya da duk masu kaunar Dimokradiya ba zasu taba mantawa dashi ba.

Baicin canza ranar Dimokradiya, kazalika shugaban Najeriya ya ba Chief Abiola lambar yabo mafi girma a kasar nan.

Sauran mutanen da gwamnatin Buhari ta ba lambar yabo sun hada da Chief Gani Fawehinmi da Ambassador Babagana Kingibe wanda ya kasance mataimakin dan takarar shugaban kasa, wato Chief M.K.O. Abiola a zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993 da aka soke.

en_USEnglish
en_USEnglish