AN BUKACI SHUGABAN KASA DA YA SANYA HOTON MARIGAYI MKO ABIOLA A JERIN KUDADEN KASAR NAN

Daraktan yada labarai na kamfen din kungiyar MKO Abiola wato, Hope ’93 MKO Abiola Campaign Organization, Obafemi Oredein, ya nemi shugaba kasa Muhammadu Buhari da ya sanya hotonmarigayi MKO Abiola a jerin kudaden kasar nan.

shugaban Babban wanda ya lashe zabe a ranar 12 ga watan Yunin 1993, a kan jerin sunayen Naira.

Oredein, ya ce shugaba Buhari ya amince da goyon bayan Abiola a mulkin demokradiya, kuma shi ya sa ya ba shi babban labar girma ta GCFR.

Ya kuma ce kamata yayi an saka hoton Cif Abiola a jikin kudin kasar nan, ba wai iya lambar yabon girman ta GCFR kadai ba za a bari.

Ya kara da cewa, ya zama wajibi ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda shawarar da gwamnatinsa ta yanke na girmama marigayi Abiola tare da sauya ranar bikin demokradiya daga ranar 29 ga watan mayu zuwa ranar 12 ga watan Yuni na kowace shekara.

 

 

 

 

en_USEnglish
en_USEnglish