GWAMNATIN JIHAR NASARAWA TA RUFE WASU MAKARANTUN FIRAMAREN JIHAR.

Gwamnatin jihar Nasarawa ta rufe wasu makarantun firamare talatin da biyar a cikin karamar hukumar Obi dake jihar, sakamakon lalatasu da aka yi yayin wani rikici da ya auku da ‘yan kabilar Tivi.

Sakataren Ilimi na karamar hukumar Obi, Ogasuwa Onuku Samuel, ne ya tabbatar da hakan yayin ganawarsa da manema labarai jiya Alhamis a ofishin sa.

Ya ce, da yawa daga cikin makarantun firamaren an rufe sune kasancewar an lalatasu yayin rikicin sannan kuma al’ummar yankin sun yi gudun hijiera daga yankin.

Sakataren ilimin Ya kuma ce,duk wasu kudaden tallafin da aka samu kamata yayi a yi amfani da su wajen bunkasa ayyukan ilimi a kudancin lardin domin gyara makarantun firamaren da aka lalata su.

Ya kara da cewa, akwai bukatar gwamnati ta sake wani tsarin don magance bambancin tsakanin bangarorin biyu don tabbatar da zaman lafiya da ci gaba wanda zai iya mayar da al’ummomin yankin da rikicin ya shafa wajan gudanar da harkokin su.

 

en_USEnglish
en_USEnglish