BABBAN SUFETON YAN SANDAN KASAR NAN IBRAHIM IDRIS YA JADDADA DOKA DA ODA KAN KOWANI DAN KASA.

Babban sufeton ‘yan sandan kasar nan Ibrahim Idris, ya ce dole ne doka tayi aiki kan kowanne dan Najeriya komai girmansa ko mukaminsa.

Ibrahim idris Ya bayyana hakan ne, yayin wani jawabi ga rukunin ‘yan sandan kwantar da tarzoma daya gudana a birnin tarayya Abuja, ya ce, aikin ‘yan sanda ne, su tabbatar da cewa kowanne dan kasa ya bi doka da oda, kuma ‘yan sanda na sane da cewa, doka tana kan kowa ne dan kasa komai girmansa.

Ya kuma yabawa ‘yan sandan kasar nan  bisa jajircewarsu wajen aiki tukuru da kuma rage aikata miyagun laifuka a fadin kasar nan.

Shugaban jami`ar Abuja Dakta Abubakar ya bayyana cewa daukar matakin da babban sufeton yan sanda yayi abu ne mai kyau, na jaddada karfin doka da oda akan kowani dan kasa.

en_USEnglish
en_USEnglish