SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI YA NUNA RASHIN JIN DADINSA BISA MARTANIN DA MINISTAN YADA LABARAI YAYI GA TSOHON SHUGABAN KASA OLUSEGUN OBASANJO.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nuna rashin jindadin sa kan martanin da Ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammad yayi ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, na cewa gwamnatin Buhari ba za ta damu da wasu zarge-zargen da ba su da ma’ana ba, daga ko wane bangare da nufin karkatar da hankalinta ga ayyukan da ta ke.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne yayin ganawa da mambobin kungiyar da ke goyon bayansa wato (Buhari Support Organisation BSO) a fadarsa a Abuja.

Ya kuma  ya kara da cewa ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Muhammad “ya saba ma shi” a martanin da ya mayar wa Obasanjo, amma kuma ya yaba da yadda aka mayar da martanin.

A ranar Juma’ar data gabata ne tsohon Shugaban kasa Obasanjo, ya fitar da sanarwar zargin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da kokarin kama shi.

Mista Obasanjo ya ce gwanatin Buhari na tattara shaidun boge domin ta daure shi saboda sukar da yake wa shugaban, inda ya ce rayuwarsa na cikin hatsari domin an kwarmata ma sa cewa, yana cikin jerin sunayen mutanen da ake farauta.

Kafar sadarwa ta BBC ta rawaito cewa Shugaba Buhari ya ce “martanin da ministan ya mayar ya nuna wa ‘yan Najeriya ainihin abin da ya faru a lokacin da suka karbi mulki a 2015 da kuma kokarin da gwamnatin sa ke yi na farfado da tabarbarewar tattalin arzikin da ta gada.

 

en_USEnglish
en_USEnglish