SHUGABA BUHARI YA MIKA LAMBAR YABO TA GCFR GA IYALAN MARIGAYI CHIEF MKO ABIOLA.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ‘Yan Nigeria da su karbi sabon sauyin da gwamnatin Nigeria ta yiwa ranar dimukradiyya yiwa da zuciya daya tare da yi masa kyakkwar fahimta.

Shugaban ya ambata haka ne yau a Abuja a yayin taron tabbatar da sauyin ranar dimukradiyya daga ranar 29 ga watan mayu zuwa 12 ga Yunin kowacce shekara, domin girmama marigayi M.K.O Abiola wanda akace na hanyar lashe zaben shugaban kasa daya gudana a shekarar 1993.

Shugaba Buhari ya kuma ce anyi sauyin ne domin a kawar da dukkan wata damuwa da kuma dinke duk baraka tsakanin al’uma kana da kuma tabbatar da hadinkan kasa.

A yayin taron, shugaba Buhari ya mika shedar karramawa ga marigayi M K O Abiola wadda dansa Kola Abiola ya karba da kuma Bababa Gana Kingibe wanda ya kasance dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben na shekarar 1993 da kuma sauran wasu muhimman mutane masu jibi da gwagwamayar zaben karkashhin tsohuwar jam’iyyar SDP.

en_USEnglish
en_USEnglish