AN YANKE HUKUNCIN KISA GA WASU MATASA BIYAR.

Wata kotu dake zaman ta a birnin Yolan jihar Adamawa ta yankewa wasu matasa biyar hukuncin kisa bisa samun su da laifin kashe wani makiyayi da suka yi da kuma farwa shanun su.

Mai shari’a Abdul Azeez Waziri ya ce masu laifun Alex Amos da Alheri Phanuel da Holy Boniface da Jerry Gideon da kuma Jari Sabagi dukannin su mazauna garin Demsa ne kuma an same su da aikata laifin ne tun a ranar 1 ga watan Yuni shekarar 2017 a wani kauye dake Kadamun dake karamar hukumar Demsa.

Ya ce matasan karya doka na cikin kundin penal code sashe na 96 daya cikin baka A cikin baka da kuma sashe na 79 da na 221 B cikin baka.

Matasan an dai same su ne da laifin farwa makiyayan su uku sannan kuma suka kashe daya daga cikin su mai suna Adamu Buba sannan suka cillashi cikin ruwa tare da shanun da suka kashe.

A don haka ne mai shari’a Abdulazeez Waziri ya yankewa uku daga ciki hukuncin kisa ta hanyar rataya sannan biyu daga cikin su hukuncin zama a gidan yari na tsawon shekaru uku.

Sai dai kuma alkalin ya baiwa matasana kwanaki 90 domin basu damar daukaka karar zuwa kotun kauli.

 

en_USEnglish
en_USEnglish