MAJALISAR ZARTARWA TA SANYA HANNU KAN FADADA TITIN ILORIN.

Majalisar Zartarwa ta gwamnatin tarayya ta sa hannu kan fadada aikin titin Ilorin zuwa Jabba zuwa Mokwa akan kudi naira biliyan dari da talatin a cigaba da manyan ayyuka da gwamnatin ke yi domin ayyukan raya kasa.
Karamin ministan wuta lantarki, ayyuka da gidaje Mustafa Shehuri ne ya bayyana hakan bayan kammala zaman majalisar zartarwa da shuagaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Mustafa Shehuri ya ce gwamnatin ta kuma amince da aikin titi na Suleja zuwa Chaaza zuwa Banguru mai nisan kilomita goma sha 7a jihar Naija akan kudi naira biliyan biyar da miliyan dari tara.
Kazalika majalisar zartarwar ta kuma amince da aikin fadada titin Ilorin zuwa Jebba zuwa Mokwa zuwa Bokani a jihar kwara da Naija akan kudinaira biliyan dari da talatin. Sannankuma za a kammala aikin ne a watanni 36.
Sauran guraren da majalisar ta amince za a yiwa ayyuka sun hadar da aikin gada a kogin River Benue wacce ta hada jihar Taraba da Platue akan kudi naira biliyan 57.

en_USEnglish
en_USEnglish