SHUGABA MUHAMMADU BUHARI YA CE ZAI YIWA BANGAREN TSARO KWASKWARIMA.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa zata yiwa harkar tsaro kwaskwarima domin shawo kan matsalar tsaro data ke kara tabarbarwewa a kasar nan.

Shugaban kasa Muhammadu Bahari ya yi ganawa ta musamman a jiya da shugaban majalisar Dattawa sanata Bukola Saraki da kuma shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara.

Da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala ganawar shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara yace shugaba Buhari ya shaida musu cewa a ziyarar da ya kai jihar Plateu domin yin jaje ya ga irin illar da wancan rikici ya haifar don haka yake son yin kwaskarima ga harkar tsaro domin magance matsalar cikin gaggawa.

A wani rahoto da kwamitin tsaro na majaliar dattawa ya fitar a baya ya nuna cewa babu fahimtar juna tsakanin bangarorin tsaron kasar nan wajen gudanar da ayyukansu.

 

 

en_USEnglish
en_USEnglish