WATA TANKAR DAKON MAI TA KAMA DA WUTA A GARIN LEGOS.

Wata tankin dakon mai ta kama da wuta a Legas da ke Najeriya, inda jami’ai suka ce gobarar ta kashe akalla mutum tara.

Sama da motoci 50 ne wadanda suka hada da bas-bas, suka kama da wuta a lokacin da motar makare da mai ta kufce, sannan man da take dauke da shi ya malale a kan hanya.

An ce motar ta fadi ne sanadiyyar katsewar burki.

Gobarar motocin dakon mai abu ne da aka saba gani a Najeriya, wadda ita ce kasar da ta fi kowacce fitar da mai daga Afirka zuwa kasuwannin duniya.

Ana safarar irin wannan mai ne ta hanyoyin mota a kasar, wadanda ba su cika samun kulawa ba.

Gobarar ta ranar Alhamis, ta faru ne da misalin karfe biyar da rabi na yamma, a kan babbar hanyar da ta tashi daga Ibadan zuwa cikin birnin na Legas.

Gobarar ta faru ne a lokacin da al’umma da dama ke zirga-zirga

Wani jami’in hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta kasar FRSC, ya shaida wa BBC cewa motar ta kwace ne a lokaci da ta tun kari wata gada, sannan ta kife a gefen gadar.

A wannan lokaci ne mai ya rinka kwarara daga cikiin motar, abin da ya haddasa gobara, wadda ta bazu zuwa saurarn motoci.

Hotunan wurin da abin ya faru sun nuna yadda bakin hayaki ya turnuke sararin samaniyar wajen, da kuma fankon motocin da suka kone.

Hanyar Ibadan zuwa Legas na daga cikin manyan hanyoyin shiga birnin Legas

Shugaban kasar Muhammadui Buhari, ya ce ya yi bakin ciki game da asarar rayukan da aka yi.

A cikin wata sanarwa, shugaban ya ce “Wannan na daya daga cikin hadurra mafi muni da aka samu a baya-bayan nan”.

Wani mai magana da yawun gwamnati Kehinde Bamigbetan, ya ce “Lokaci ya yi da za a tabbatar da cewa mutane masu hankali ne sosai kawai suke tuka irin wadannan motoci na dakon mai.”

 

en_USEnglish
en_USEnglish