KAMFANIN MAI NA NNPC YA BADA GUDUMMAWAR NAIRA MILIYAN HAMSIN.

Kamfanin mai na kasa NNPC ya bada gudunmawar kyautar naira miliyan hamsin ga wadanda ibtila’in guguwa ya shafa a jihar Bauchi tare da lalata gidaje dubu daya da dari 5.

Daraktan manajan kamfanin, Dakta Maikanti Baru ne ya tabbatar da hakan yayin ziyarar jaje da suka kai wa sarkin jihar Bauchi, Dakta Rilwanu Suleiman Adamu a fadarsa jiya Lahadi.

Ya ce makasudin ziyarar ta su shi ne da su jajantawa al’umar yankin wadanda ibtila’in guguwar ya shafa a makwanni biyun da suka gabata

Ya kara da cewar, al’umma da dama sun rasa matsugunan su a cikin wannan ibtila’in day a faru, kuma ba za su nade hannu suna kallo haka kawai ba ba tare da bada gudunmawar sub a.

Shi kuwa a nasa jawabin maimartaba Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Suleiman Adamu, ya bayyana godiyar sa ga tallafin da kamfanin manfetur din ya bayar, sannan kuma yace kudin zasu mika shi wajan kwamatin da gwamnati ta kafa domin ganin an mika shi ga mutanen da ibtila’in ya shafa.

en_USEnglish
en_USEnglish