GWAMNAN BORNO YA GANA DA ABBA KYARI A FADAR SHUGABAN KASA GAME DA ZANGA ZANGAR YAN SANDA

Sa’o’i 24 bayan zanga zangar ‘yan sanda a birnin Maiduguri saboda rashin biyan su alawus da hakkokin su na ayyukan tsaro na musamman, yanzu haka gwamnan jihar Borno Kashim Shettima na ganawa da shugaban ma’aikata a fadar shugaban kasa a can Abuja.
A jiya litinin ne dai ‘yan sanda suka mamaye wasu tituna na birnin Maiduguri a yayin zanga zangar, inda sukace sun kwashe watanni shida kenan suna aiki babu alawus, lamarin daya jefa su cikin mawuyacin hali.
Sa’o’i kalilan bayan gudanar da zanga zangar ne, babban sifeton ‘yan sandan kasar nan yayi makamanciyar wannan ganawa da shugaban ma’aikatan a fadar shugaban kasa Alhaji Abba Kyari wanda shi-ma dan jihar Borno ne.

Sai dai har yanzu kafofin labaru ba su kai ga tantancewa, ko fadar shugaban kasar ce ta umarci sifeton ‘yan sandan ya bayyana domin bayanin musabbabin zanga-zangar ko kuma a’a.

MIK

en_USEnglish
en_USEnglish