GWAMNATIN SAKWKWATO TA BAWA DAN WASAN KWALLON KAFA TUKWICIN GIDA.

Gwamnatin jihar Sokoto ta bada kyautar gida mai dakuna hudu ga Abdullahi Shehu dan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa wato Super Eagles.
Gwamnan Aminu Waziri Tambuwal,ya sanar da haka yayin wata ziyarar ban girma da Dan wasan ya kai masa a gidan gwamnatin.
Gwamnan yace matakin ya biyo bayan bajintar da Abdullahi Shehu ya nuna a yayin gasar cin kofin duniya da ke wakana a kasar Rasha.
da yake jawabi Dan wasan Abdullahi shehu ya yabawa gwamnan bisa irin hubbasan dayake a bangaren ilimi tare da taimakawa matasa a harkokin wasanni.
Ya kara da cewa, gwamnatin Jihar ta Sokoto na kokari matuka wajen dakile ta’ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin matasan jihar ta Sokoto.

ARJ/MIK

en_USEnglish
en_USEnglish